An tarawa marayu kudi Naira miliyan talatin da biyu a inda Sheikh Kabiru Gombe yake tafsiri
A safiyar asabar dinnan kwamitin marayu na FCT Abuja ta gabatar da rabawa marayu kayan tallafi na abinci, atamfa, shaddoji da kudade gare su.
An samu kudaden ne a wajen da Sheik Kabiru Gombe yake gabatar da tafsirin watan Ramadan a masallacin JIBWIS dake unguwar Utako dake birnin Abuja
An fara tafsirin ne a ranar biyu ga Ramadan dinnan, zuwa azumi 21 an tara adadin kudade har naira miliyan (32,000,000.00). An sayi kayan abinci, turamen zani, da shaddoji an rabawa marayu a helkwatar Izalah tare da baiwa kowanne maraya naira dubu biyar (5,000.) kudin dinki.
Sannan an dauki nauyin karatun marayu yara 100. An dauki nauyin aurar da 'yan mata marayu guda 20, kowacce za a kashe mata dubu dari uku (300,000) wurin yi mata kayan daki, sannan za a koya musu sana'a.
A wannan hidimar an kashe wadannan kudaden har sai da Sheik Bala Lau yayi cikon milyan biyu.
JIBWIS NIGERIA