Naziru Sarkin Mahaukata Ne, Ba Sarkin Mawaka Ba: Babanchinedu Ya Yiwa Naziru Wankin Babban Bargo Kan Nafisa Abdullahi
Babban jarumin Kannywood, Babanchinedu ya shigo cikin fadan abokan sana'arsa Naziru Ahamad wato Sarkin waka da Nafisa Abdullahi.
Babanchinedu ya caccaki Naziru sarkin waka kan kalaman da ya yi game da jaruma Nafisa saboda ta kalubalanci tura yara almajiranci, ya bayyana cewa akwai son zuciya a maganar tasa.
Jarumin ya ce ba komai bane ke damun sarkin waka face haushin cewa Nafisa ta bar masu fim dinsu na 'Labarina' saboda zaluncin da aka nuna mata.
A cikin wani bidiyo da ya saki a shafinsa na Instagram, ya bayyana mawakin a matsayin 'sarkin mahaukata' wanda ya dauki girman kai da izza ya daura wa kansa.