YACIE HAKAN YA FARU

April 25, 2022
3 years ago

Zuciyar Almajirai A Kekeshe Take Ba Suda Tausayi ~ Dr Rabi'u Musa Kwankwaso

 

Daga Usman Rabiu Kwankwaso

 

Dr Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana almajirai a matsayin masu kekeshashen zuciya, marasa tausayi.

 

Yace hakan ya faru sakamakon rashin kulawa da iyayen su basu basu ba, babu wani investment a jikin su.

 

Dan haka ne ma basa tausayin kowa, shi yasa sai su harbe mutum, in aka cika takura musu ma sai su harbe kansu.

 

Tambayata ga Kwankwaso da kuma 'yan kwankwssiyyan dake kokarin kare kwankwaso akan wannan zancen da yayi, shin zamu iya sanin wani almajiri ne suka san ya harbe kan shi da kan shi? 

 

Wasu almajirai ne yaji suna kashe mutane kuma a ina?

 

Ina tabbatar muku da ace wani malamin addini yayi wannan maganar da yanzu bai iya hawa media ba a wajan yan kwankwasiyya da yanzu jaridun hausa da muke dasu a facebook sun gama ca akan malami, amma da ike wanda baya kuskure ne a wajan su kaji su sunyi tsit, ji maganar nafisa abullahi yadda akai.

 

Kafin wani ya karyata ni yaje ya kalli video din da yayi maganar.