WATA RANA

April 26, 2022
3 years ago

Wata rana Sahabban manzon ALLAH (S.W.A) sun kawo karar SAYYIDINA ABUBAKAR gurin Manzon Allah (S.A.W) suna Cewa Ya Manzon Allah: Abubakar ya kasance idan muka hadu dashi yana riga bamu hannunsa muyi musabaha cikin farin ciki da sakin fuska. Amma yanzu idan muka hadu dashi sai ya sunkuyar da kansa kasa sai mun fara bashi hannun mu sannan zai miko nasa. Sai Manzon Allah (S.A.W.) yace aje maza a kira Sayyidina Abubakar, cikin lokaci sai gashi yazo, yana zuwa sai Manzon Allah (S.A.W) yace kaji abin da Sahabbaina suka fada, gaskiya ne? Sai Sayyidina Abubakar cikin girmamawa yace: Ya wanda bakinsa baya karya, Eh hakane gaskiya ne suka fada. Amma ina da hujja, sai yace jiya nayi mafarkin wani katafaren gida wanda babu abinda ke cikinsa sai kayan alfarma da more rayuwa da jin dadi wani abin ma hankali da tunani baya misalta su, Allah (S.W.T) ya fadamin cewa: "Babu wanda zai shiga wannan gidan face Wanda idan ya hadu da mutane yana riga mika musu hannu domin a gaisa kuma cikin sakin fuska da murmushi", to shine nake musu kwadayin wannan gida dasu shigeshi, shi yasa na bari su rinka fara miko min hannunsu suna farin ciki da sakin fuska da murmushi. Allahu Akbar !!! Don Allah dan uwa Kada Ka Karanta ka barshi kai kadai, ka turawa 'yan uwanka Musulmai Masoya Manzon Allah (S.A.W). Jama'a don girman Allah Ku bada minti 2 domin karanta wannan babban sako; Manzon Allah saw yana cewa: Ku yawaita yin salati a gareni domin salatinku a gareni to haskene a gareku ranar tashin Alqiyama, ya Kara da cewa mutanen dake zaune a fadata ranar tashin Alqiyama sune masu yawan yimun salati, ya Allah muna rokonka da sunayenka 99 tsarkaka, ya Allah dan Sittin na Alqurani, ya Allah dan darajar Gadon Al-Arshi duk Wanda ya tura wannan sakon ga yan uwa musulmi Allah kaji kansa, ka gafartamasa kurakuransa, ka daukakashi akan makiyansa ya Allah duk bukatunsa na alkhairi ka biyamasa ya Allah ka tayar dashi a fadar manxon Allah saw ranar tashin Alqiyama, daga karshe ka sakashi Aljanna Madaukakiya,

 

Ameen....