YA KAMATA SHUGABAN NDLEA BUBA MARWA YA BINCIKI YARONSA SUNDAY ZIRANDI
Hukumar NDLEA ta fitar da sanarwa akan wani babban attajiri dan kasuwa da ta kama mai suna Chief Ukatu wanda take zargi da sayar da kwayar Tramadon na Biliyoyin Naira, abin mamaki sai a rahoton NDLEA ta sanya sunan DCP Abba Kyari, alhali shi Chief Ukatu bai taba ambatar sunan Abba Kyari ba, kuma babu wata alaka tsakaninsu
Chief Ukatu dukkan sauran wadanda ake zargi a yanzu da a baya babu wanda ya taba ambatar sunan Abba Kyari, bukumar NDLEA da gayya take kokarin kulla alaka tsakanin masu safaran kwayoyi da Abba Kyari ba tare da suna da wata shaida kwakkwara ba, jami'an IRT da suka kama masu safaran kwayoyi a Lagos suna transfer case zuwa NDLEA babu wani cikin jami'an da ya taba ambatan sunan Abba Kyari a cikin case dinsu, babu kudi ko kobo daya da kwaya ko katon daya da aka samu a gurin Abba Kyari
An fara case din Chief Ukatu aka kammala a Lagos ba tare da DCP Abba Kyari yana gurin ba, shi wannan jami'in NDLEA Sunday Zirandi da yake Lagos a lokacin wanda yaci amanar Abba Kyari shine yake ta kokarin ya lika masa wannan case din ba tare da yana da wata shaida ba
Idan NDLEA ta isa tana da kuma shaida, to ta gabatarwa duniya bayanan Chief Ukatu inda ya ambaci sunan Abba Kyari ko wani abu makamancin haka akan wannan sabon rahoton karya da NDLEA ta fitar akan case din Chief Ukatu
Dukkan asusun ajiyar kudin banki na DCP Abba Kyari da mataimakinsa babu kudin da ya kai sama da Naira Miliyan 3 a ciki, amma haka NDLEA suka fitar da rahoto na karya suka sanar wa duniya cewa sun gano kudi sama da Naira Biliyan 4 a cikin Bank accounts dinsu, idan NDLEA suna da gaskiya to su fitar da bayanan asusun ajiyar kudin Abba Kyari na banki duniya ta gani ko gaskiya ne abinda suka wallafa, amma me yasa NDLEA take ta fitar da rahoton karya akan wadannan jaruman 'yan sanda?
Duk abinda NDLEA take fadi akan makudan kudaden da ta fitar da rahoton karya tace ta gano a account din Abba Kyari da na mataimakinsa karya ne kawai da sharri, akwai sauran hukumomin tsaro da suka gudanar da bincike da sauran ma'aikatan banki duk sun duba ba su ga wannan kudin ba, babu wani kudi makamancin haka da ya taba shiga cikin Bank Account na Abba Kyari da mataimakinsa, kudin dake cikin account din Abba Kyari an gano bai kai ko Naira Miliyan 3 ba, don Allah ku kalubalanci hukumar NDLEA ta fitar da statement of Account na Abba Kyari idan sun taki gaskiya
Amma me yasa hukumar NDLEA take ta fitar da rahoton karya da batanci akan DCP Abba Kyari mutumin da ya sadaukar da rayuwarsa yayi yaki da wadanda suke neman wargaza zaman lafiyar Nigeria? jami'in dan sanda daya tilo wanda ya samu lambar yabo daga Shugaban Kasa da majalisar Dattawa da lambar yabo har sau 3 daga shugaban 'yan sanda na kasa IGP, da sauran lambobi na yabo da kwazo da ya samu??
Me yasa NDLEA ta bari Sunday Zirandi yake ta shirya wa DCP Abba Kyari sharri da makirci haka, yana ta bata masa suna bayan sun kaishi kotu? me yasa NDLEA take yiwa Abba Kyari haka? me yake faruwa ne a Kasar nan aka kyale wasu wawaye suna kokarin su ruguza kwararren jami'in tsaro wanda babu irinsa a Nigeria? ~ Barr Olatunde Kehinde
Muna amfani da wannan damar wajen jawo hankalin Maigirma Shugaban hukumar NDLEA Babu Marwa, lallai ka binciki jami'inka Sunday Zirandi, muna zargin wakilan IPOB sun bashi kwangila a boye domin su yi ramuwar gayya akan abinda DCP Abba Kyari ya yiwa mayakansu, Sunday Zirandi zai zama sanadi na bata maka tarihi a duk ranar da gaskiya ta bayyana
Muna rokon Allah Ya bayyana da gaskiya, Ya tozarta duk wani azzalumi maciyin amana