MU'UJIZAR ANNABI (SAW)TASA ANYI RUWAN SAMA
dan Allah kayimin alfarman tura wannan rubutu cikin wasu groups
Sayyiduna Umar (r'a) Yana cewa: mun Fita Zuwa Yakin Tabuka tare da Annabi (s a w) A lokacin da ake cikin Tsananin zafi mai kuna. Mun ya da Zango a wani wuri. Kishi ruwa ya dame mu.
Mutum ya kan fita don ya nemi ruwa. Kafin ya dawo Sai ya ji makogoronsa kamar ya tsatsage. Wasu Sukan yan ka ragumi su ciro tumbinsa su sha Ruwan..
Sai Sayyiduna Abubakar Saddik (r'a)Yace muna Roqan ka da kayi Mana adda'a.
Sai Annabi (s a w)Ya daga hannayensa sama yana adda'a. Aikuwa Kafin ya Sauke hannayensa masu Daraja. Sararin sama ya Chanja haddari ya hado ruwa ya tsainke. Mutane suka sha suka cika Abubuwan da ke tare da su.
Muka duba Sai mukaga Ruwan a iya inda muke kadai Akayi shi.
Dan gane. Aduba a Tafsirin Dabri. 14 \541. Ibn Hibban. Hadisi mai number 1707. Hakim. :juz'i na daya. 159. Ya kuma inganta shi da Shi da Ibn kathir.
Pls idan baka cikin wannnan page kayi like and following kaciga
Dan girman Allah kayi share zuwa groups 5 Don Su ma Sa amfana da kai